ABNA24 : Shugaban tawagar ta Iran ta kuma kara da cewa; Mun cimma matsaya akan muhimman batutuwa, sai dai ba za mu iya yanke cewa mun kai ga cimma matsaya akan kowane daga cikinsu ba, sai dai ina da tabbacin cewa a wannan karon tattaunawar za mu iya samun ci gaba ko kuma ma kammala tattaunawar.
Da yake amsa tambaya akan ko daya bangaren da ake tattaunawa da su, suna da azamar siyasa akan batun, Araqchi ya ce; Ba mu dade da bude wannan tattaunawar ba, don haka lamarin yana da bukatuwa da yin nazari na wasu kwanaki masu zuwa. Sai dai abinda na lura da shi, da akwai azama daga kowa domin cimma matsaya.
342/